Dangane da wannan lamari, kasashen Koriya ta Kudu da Rasha da Amurka da Sin, har ma da babban magatakardan MDD suka bayyana bacin ransu, inda suka yi kira ga Koriya ta Arewa, ta yi biyayya ga kudurin kwamitin sulhu na MDD tare da warware sabanin dake tsakaninta da bangarori daban- daban a siyasance.
Haka zalika, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa a jiyan, inda ya yi allah wadai da gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi, inda ya ce matakin ya bata ran gamayyar kasa da kasa.
Bugu da kari, bisa kiran da zaunannannun wakilan kasashen Amurka da Japan suka yi a jiya da yamma, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taron tattaunawa kan gwajin makamin na Koriya ta Arewa.
Bayan taron ne kuma aka fitar da wata sanarwa da ta yi Allah wadai da kakkausar harshe kan harba makamin, tana mai bukatar kasar ta dakatar da gwajin da take yi ba tare da bata lokaci ba. (Maryam)