Da yake karin haske game da batun shirin gwajin makaman nukiliyar DPRK wanda ya bayyana shi a matsayin barazana ga tsaro da zaman lafiyar duniya, mista Trump ya shedawa 'yan jaridu cewa, sabuwar dokar da ya rattabawa hannu zata taimaka wajen rage adadin kudaden shigar da DPRK ke samu wadanda da su ne take aiwatar da shirinta na kera makaman nukiliyar.(Ahmad Fagam)