Kalaman nasa na zuwa ne bayan da shugaban kasar Koriya ta kudu Moon Jea-in ya ba da shawarar cewa, kasarsa za ta ci gaba da shirinta na kai kayayyakin agaji Koriya ta arewa, duk da takaddamar siyasar da suke ciki. Yayin da shi kuma Firaministan kasar Japan Shimzo Abe ya bukaci a samu lokacin da ya dace na kai wadannan kayayyaki.
Mr. Lu Kang ya shaidawa taron manema labarai cewa, dukkan kudurorin da kwamitin sulhu na MDD ya yanke game da kakabawa koriya ta arewan takunkumi, ciki har da sabon kudurin da kwamitin ya amince da shi mai lamba 2375, ba su da nufin yin illa ga rayuwar fararen hula da masu bukatar jin kai dake kasar.
Ya ce alummar kasashen biyu, kabilarsa daya, kuma har kullum kasar Sin tana goyon bayan kasashen biyu su karfafa yin musaya da hadin gwiwa da kuma sassantawa a tsakaninsu.(Ibrahim)