Masu zuba jari na kasar Sin sun ce nahiyar Afrika za ta iya jan hankalin karin masu zuba jari idan ta samar da yankunan hada-hadar tattalin arziki na musammam.
Shugaban kamfanin Guangdong New South na kasar Sin Zhu Layi, ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na Xinhua a jiya cewa, irin wadannan yankuna na bada wasu damammakin samun rangwamen haraji, wanda zai ja hankalin masu zuba jari daga kasar Sin dake son kafa harkokin kasuwanci a Afrika.
Zhu Layi ya kara da cewa, yankunan na da mutukar muhimmanci domin za su sanya kamfanonin kasar Sin kafa masana'antun sarrafa kayayyaki a kasashen nahiyar.
A jiya Jumma'a ne kasar Kenya ta kaddamar da aikin samar da yankin hada-hadar tattalin arziki na musammam, wanda na hadin gwiwa ne tsakanin wani kamfanin kasar Kenya mai sun Afrika Economic Zone da Guandong New South, inda ake sa ran zai samarwa Kenya jarin dala biliyan 2 daga masu zuba jari na kasashen waje.
Masana na kasar Kenya sun ce yankin zai taimaka wajen rubanya ayyukan sarrafa kayayyaki da kusan miliyan 1, inda alkaluman tattalin arziki na GDP za su kai dala biliyan 2 zuwa 3 cikin shekaru goma masu zuwa.
Ana alakanta saurin bunkasar harkokin masana'antu a kasar Sin cikin shekaru 30 da suka gabata da kyakkyawan amfani da yankunan hada-hadar tattalin arziki na musammam.
Kasar Sin ta yi amfani da yankunan wajen inganta habakar masana'antu tare da cimmar gasar da ake a duniya a wannan bangaren. (Fa'iza Mustapha)