Wata sanarwa da aka fitar a jiya, ta ce hukumar ta yi wannan kira ne yayin bude taro kan bada taimako wajen sake fasalin harkokin cinikayya a duniya na 2017, wanda ya gudana a hedkwatar hukumar kula da harkokin cinikayya ta duniya WTO dake Geneva na kasar Switzerland.
Da yake jawabi yayin taron, Darakta a sashen bunkasa ayyuka na ECA Stephen Karingi, ya jadadda bukatar bunkasa cinikayya a tsakanin kasashen Afrika, wanda a yanzu ya tsaya kan kashi 13 cikin 100 na jimilar harkokin cinikayya a nahiyar.
Stephen Karingi ya ce, abun da ECA ke nufi shi ne, akwai bukatar gwamnatocin Afrika su kara zage damtse wajen inganta cinikayya a tsakaninsu, ya na mai alakanta karancin harkokin kasuwanci tsakanin kasashen da rashin cudanya da juna da na isassun hanyoyin sufuri a fadin nahiyar.
A don haka, ya ce ya kamata a yi tunanin inganta hanyoyi sufuri da sauran ababen more rayuwa inda aka fi samun gagarumin gibi. (Fa'iza Mustapha)