Antonioa Guterres ya yi wannan kira ne yayin bikin ranar agajin jin kai ta duniya dake gudana a ranar 19 ga watan Augusta.
Ya ce kare fararen hula a lokacin rikici abu ne mai wahalar aiwatarwa. Sannan abu mafi muni shi ne yadda ake kara kai hare-hare kan masu bada agajin jin kai, baya ga rashin darajar tutar Majalisar, wanda alama ce dake nuna cewa ba ta nuna fifiko ga wani bangare dake rikici.
Har ila yau, Sakataren na MDD ya ce kare fararen hula yayin da ake rikici muhimmin abu ne cikin dokar agajin jin kai ta duniya. Sai dai, a fagen yaki a duk fadin duniya, bangarorin dake rikici na take wannan doka, inda ake ci gaba da kai hare-hare tare da kashe fararen hula, yana mai cewa, ba a dauki ran dan Adam a bakin komai ba. (Fa'iza Mustapha)