Mr. Wane wanda ya gabatar da jawabi gaban zauren kwamitin na tsaron MDD a jiya Talata, ya ce yanzu haka tawagar hadin gwiwa ta dakarun kungiyar kasashen yankin na Sahel ta G5, wadda ta kunshi sojojin kasashen Mali, da Mauritania, da Nijar, da Burkina Faso da Chadi, na iyakacin kokarin murkushe ayyukan mayakan sa kai a yankin.
To sai dai kuma a cewarsa, ayyukan 'yan ta'adda na haifar da babban kalubale a yankin, kuma alakar bangarorin irin wadannan kungiyoyi da juna, na haifar da barazanar rashin daidaito, da ci gaban yankin baki daya.
A daya bangaren kuma a cewar jami'in, hadin gwiwar G5, ya bude wata kofa ta magance tarin kalubalen da wannan yanki ke fuskanta, inda shirin kungiyar ke samar da kudade, da dakaru, da horo da kayayyakin aiki da dai sauran su.
A ranar 2 ga watan Yuli ne shugabannin kungiyar ta G5, da hadin gwiwar kasar Faransa, suka kaddamar da rundunar musamman domin cimma burin wanzar da zaman lafiya da lumana a daukacin yankin na Sahel. (Saminu Hassan)