Sakatare janar din ya bayyana hakan ne bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar na ranar Talata, inda hukumomin zaben kasar Kenyan suka ayyana shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben.
Guterres, ya bukaci shugabannin siyasar kasar da su gaggauta yin kira ga magoya bayansu da su datakar da tashin hankalin. Sakatare janar din ya nanata muhimmancin tattaunawar sulhu domin kawo karshen zaman tankiya a kasar.
MDD, da kungiyar tarayyar Afrika, da sauran abokan hulda, sun tsaya tsayin daka inda suke gudanar da aiki tare da masu ruwa da tsaki da shugabannin siyasar kasar Kenyan domin tabbatar da ganin an aiwatar da zaben kasar cikin nasara.
An kashe mutane a kalla 20 a rikicin bayan zaben kasar ta Kenya sakamakon zargin da bangaren 'yan adawar kasar ke yi na tafka magudi a zaben inda suke zargin an fifita bangaren mista Kenyatta.(Ahmad Fagam)