Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, wanda ya yi kiran a jiya, ya ce Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da arewa maso gabashin Nijeriya, na fama da kalubalen 'yan ta'adda da kungiyoyi masu dauke da makamai, al'amarin da ya jefa tsaro a wuraren cikin matsanancin yanayi, inda mata da yara ke cikin hadarin fuskantar fyade.
Wu Haitao ya shaidawa wani taron kwamitin sulhu na MDD cewa, ya kamata al'ummomin kasashen waje su kara mai da hankali kan wannan batu, tare da inganta kare mata da yara masu rauni.
Ya yi kira da a yunkura wajen daidaita yanayi tare da inganta tsaro.
Wakilin na kasar Sin ya kuma gargadi al'ummomin na ketare, su tsaya kan turbar sulhunta batutuwa a siyasance tare da ba bangarori masu adawa kwarin gwiwar sulhunta rikicinsu cikin kwanciyar hankali ta hanyar tattaunawa da cimma yarjejeniyoyi.
Ya kuma bukaci a kara kokari wajen magance matsalar ta'addanci da laifuffukan da ake aikatawa a kan iyakoki, domin datse kwararar 'yan ta'adda da samar da kariyar da ake bukata da kuma bada agajin jin kai ga mata masu rauni. (Fa'iza Mustapha)