Da yake ganawa da manema labarai jiya a hedkwatar Majalisar dake birnin New York, Antonio Guterres ya ce daukacin kwamitin Sulhu na majalisar ya amince da kuduri mai lamba 2371 a ranar 5 ga wannan watan. Yana mai cewa kudurin ya aike da sako a bayyane game da zaman lafiya da tsaro da ya kamata Koriya ta arewa ta kiyaye.
Musamman zaman dar-dar game da batun zirin Koriya wanda ya kai wani mataki da ba a taba gani ba, yana mai cewa suna tunawa da mawuyacin hali da yakin Koriya da aka fara yau da shekaru 67 da suka gabata ya haifar.
Sakatare Janar din ya kuma jadadda cewa, yakin Koriya wanda ya shafi kasashe da dama tare da haifar da dimbin asarar, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da miliyan 3.
Antonio Guterres ya ce akwai bukatar daukar darasi daga tarihi, domin kaucewa maimaita kuskuren. (Fa'iza Mustapha)