Rahoton ya ce, kungiyar Al-Nusra Front wadda ta kai harin, kungiyar ta'addanci ce, kuma ya kamata gamayyar kasa da kasa su yi allah wadai kan dukkan hare-haren ta'addanci ba tare da bata lokaci ba.
Rahoton ya kara da cewa, mambobin kwamitin sulhu na MDD da suka hada da kasashen Amurka, Burtaniya, Faransa da Ukraine da sauransu, sun hana Rasha ta gabatar da bukatarta na yin kira ga kwamitin sulhun ya fitar da sanarwar Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancinta dake Syria.
A ranar 2 ga watan nan ne, aka kai harin bomabomai kan ofishin jakadancin Rasha dake birnin Damascus na Syria, amma babu wanda harin ya rutsa da shi.
Rasha dai ta yi kira ga mambobin kwamitin sulhu na MDD su yi tir da harin da 'yan ta'adda suka kai kan ofishin jakadancinta. (Maryam)