Mr. Shifeta ya ce, tuni ma'aikatar harkokin kare muhalli da yawon shakatawa ta nemi wasu matukan jirgin sama, wadanda za su fara ayyukan sintiri a lambun shan iska na kasar dake Etosha, da kuma lambun shan iska na kasar dake Babatwa.
Bisa kididdigar da ma'aikatar muhalli da yawon shakatawa ta yi, an ce a shekarar 2014 kadai, an sace karkanda guda 61, da wasu guda 91 a shekarar 2015, kana da karin wasu 63 a shekarar 2016.
A sa'i daya kuma, an sace giwaye guda 78 a shekarar 2014, da wasu 49 a 2015, tare da karin wasu 101 a shekarar 2016. Kuma an sace galibinsu ne daga lambunan shan iska na Etosha da na Babatwa. (Maryam)