Yau Alhamis 13 ga watan nan ne mataimakiyar firaminista, kana ministar harkokin wajen kasar Namibia Netumbo Nandi-Ndaitwah, ta bayyana a yayin taron manema labaran da aka yi a birnin Beijing cewa, kasar ta na maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin, da kuma shigarsu cikin ayyukan ginin kasar ta Namibia.
Tun dai ranar 10 ga watan nan ne Mrs. Ndaitwah ya fara ziyarar aiki a hukunce a nan kasar Sin, bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi mata. A yau ne kuma ake sa ran za ta kammala wannan ziyara. (Maryam)