Daraktan zartarwa na shirin kare muhalli na MDD (UNEP) Erik Solheim, ya yi kira ga duniya baki daya, da a hada hannu wajen yaki da guguwar kura da kasa.
Erik Solheim ya bayyana haka ne jiya a birnin Tehran, lokacin da yake ganawa da kamfanin dillanci labarai na Xinhua, a wajen taro kan kalubale da mafita game da matsalar guguwar kura da kasa, wanda shirin UNEP ya kaddamar da hadin gwiwar ma'aikatar muhalli ta Iran.
Daraktan ya ce, ya kamata dukkan kasashen duniya su hada hannu wajen samar da mafita domin yaki da guguwar kasa, da nufin kare lafiyar al'umma da tattalin arziki da kuma samar da muhalli da zai dace da rayuwa.
Nasarar da kasar Sin ta samu na sake farfado da daji a babban saharar dake haifar da guguwar kasa a kai a kai a yankin Kubuqi, ya samar da dabaru ga sauran kasashe dake fama da lalacewar dazuka.
Erik Solheim ya ce, UNEP na aiki da kasar Sin wajen ganin an kulla kawance da sassan duniya wajen inganta kare muhalli karkashin shawarar ziri daya da hanya daya domin inganta amfani da makamashin da ake iya sabuntawa. (Fa'iza Mustapha)