Da yake jawabi game da halin da kasar ke ciki a gaban majalisar dokokin kasar, Hage Geingob, ya alakanta rashin ayyukan yi da yadda aka fi zuba jari a bangarorin hakar ma'adainai da manyan kamfanoni da suka fi amfani da injuna.
Ya ce a yanzu adadin rashin aikin yi a kasar ya kai kashi 39.2 cikin dari.
Shugaban kasar ya ce wani muhimmin matakin da gwamnati ta dauka na magance rashin aikin yi a tsakanin matasa shi ne, inganta ba da horo kan sana'o'in hannu da fasahohi.
Ya ce a bara, sama da dalibai 24,000 ne aka dauka a cibiyoyin koyar da sana'o'i, adadin da ya zarce 16,000 da aka yi niyyar dauka. (Fa'iza Mustapha)