A yayin taron, mataimakin magatakardan MDD, kana shugaban hukumar kiyaye muhalli ta MDD wato UNEP Erik Solheim ya yabawa kasar Sin kan yadda take gudanar da aikin a yankin hamadar Kubuqi, lamarin da ya janyo hankulan wakilan kasa da kasa.
Mr. Solheim ya yi bayani cewa, gwamnatin kasar Sin ta dukufa kan aikin yin rigakafi kan hadarin rairayi da kurar kasa, inda ta samun dabaru da dama wadanda za su kasance abin koyi ga kasashen duniya.
Fadin yankin hamadar Kubuqi ya kai sama da muraba'in kilomita dubu 10, fadinsa ya kasance matsayi na 7 cikin dukkan hamadar kasa ta Sin. Kuma hukumar UNEP ta mai da yankin a matsayin abin koyi ga kasa da kasa, bisa kokarin da aka yi wajen kyautata muhallin yankin hamada. (Maryam)