Wasu alkaluma da bankin raya ci gaban Afrika ADB ya fitar sun nuna cewa, ana sa ran tattalin arzikin kasashen Afrika zai farfado da kashi 3.4 bisa 100 a shekarar 2017, da kuma kashi 4.3 bisa 100 a shekarar 2018 maimakon karin kashi 2.2 bisa 100 da aka dinga samu a shekarun baya.
A cewar hasashen tattalin arzikin Afrika na shekarar 2017 wanda bankin ya fitar a ranar Litinin, yiwuwar samun bunkasuwar tattalin arzikin na Afrika ya ta'allaka ne da farfadowar da za'a samu na farashin kayayyaki a kasashen wanda zai bunkasa tattalin arzikin duniya da kuma na kasashen na Afrikan.
A cewar mai rikon daraktan shirin bunkasa tattalin arziki da hasashe da kuma bincike na bankin na ADB, Abebe Shimeles, ko da yake rikicin tattalin arzikin da aka fuskanta a shekaru biyun da suka gabata ya sauya fasalin yanayin tattalin arzikin nahiyar, amma har yanzu tattalin arzikin nahiyar yana da karfi, ya ce, idan ya kasance ba'a dogara kan wani nau'i guda na tattalin arziki, hakan zai samar da bunkasuwa da kuma karfin tattalin arzikin kasashen.
Bankin ya ce, karuwar tattalin arzikin Afrika ya ta'allaka ne da irin albarkatun da suke samarwa a cikin gidan, kamar yadda ake samun sauye sauye wajen hada bukatun da hukumomi masu zaman kansu suke da su da kuma na gwamnati, wanda ya kai kashi 60 cikin 100 a shekarar 2016.
Ci gaban ya zo daidai da ci gaban rayuwar jama'a, kasashen Afrika 18 sun samu matsakaicin ci gaban bil adama zuwa shekarar 2015.(Ahmad Fagam)