in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yankin yammacin Afrika na bukatar baza-komar tattalin arzikin domin cimma manufar zama yankin na biyu dake amfani da takardar kudi na bai daya.
2017-05-06 12:19:58 cri

An bayyana tsarin baza-komar tattalin arziki a matsayin hanyar da kasashen yammacin Afrika za su bi wajen cimma burin kungiyar raya tattalin arzikin yankin na samar da tsarin amfani da takardar kudi na bai daya.

Sakataren zartarwa na kungiyar manyan bankunan kasashen Afrika Papa Lamine Diop ya bayyana jiya bayan kammala wani taron karawa juna sani na kungiyar cewa, rashin tabbas da tattalin arziki ke fuskanta ne babban tarnaki ga samar da yankin mai amfani da tsarin takardar kudi na bai daya.

Kasashe masu amfani da harshen Turanci da suka hada da Ghana da Nijeriya da Saliyo da Gambia da Liberia da kuma Jamhuriyar Guinea mai amafani da harshen Faransanci sun shafe shekaru kusan ashirin suna aiki ba tare da samun nasara ba, wajen samar da yanki na biyu mai amfani da takardar kudi na bai daya, baya ga kasashe masu amfani da harshen faransanci dake amfani da takardar kudi na CFA.

Wannan wani bangare ne na samun hadin kan wani yanki na Afrika da zai kai ga dunkulewar tattalin arzikin nahiyar baki daya.

An yi hasashen kasashen shida za su cike wasu ka'idoji hudu da suka shafi tattalin arziki ta fuskar rage tsadar farashin kayaki a karshen shekara, sannan kudaden da kasa za ta kashe ba zai fi kudaden shigarta da kashi 4 na alkaluman GDP ba da sauransu.

Masanin ya kuma bukaci a yi amfani da kudaden da ake samu daga albarkatun nahiyar wajen kara zuba jari a bangaren noma, kasancewarsa muhimmin bangare na raya tattalin arziki a nahiyar. ( Fa'iza Mustapha) .

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China