in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala taron koli kan tattalin arzikin Afrika, inda aka yi kira da samun ci gaba na bai daya
2017-05-06 12:54:50 cri

An kammala taron koli na yini uku kan tattalin arzikin Afrika jiya Jumma'a a birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu, inda aka tattauna kan batutuwa da suka shafi samar da ci gaba na bai daya da cinikayayya tsakanin kasashen Afrika da kuma amfani da dabarun habaka tattalin arziki na zamani.

A jawabinsa yayin rufe taron, Mataimakin shugaban kasar Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya ce an cimma matsaya kan tinkarar kalubale tare da yin amfani da damammakin da nahiyar ke da su, inda ya ce an amince a gaggauta kawar da matsalolin da suka hada da wariya da rashin daidaito da kuma rashin aikin yi.

Ya ce yayin taron masu ruwa da tsaki daban-daban sun jaddada cewa, akwai bukatar dora nahiyar kan tafarkin samun dawwamammen ci gaba na bai daya cikin sauri, yana mai cewa ba kadai gajiyar ci gaban al'ummar yankin za su ci ba, har ma da shiga a dama da su cikin harkokin habaka tattalin arziki.

Ya ce sakamakon taron zai sauya Afrika daga nahiyar mai buri zuwa wadda ta cimma manufofinta.

Cyril Ramaphosa ya kara da cewa, dole ne a shirya matasa ta yadda za su fuskanci kalubalen da duniya ke fuskanta tare da kokari wajen raya tattalin arziki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China