Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bukaci kasashen nahiyar Afrika da su yi magana da murya guda don mika bukatar neman karin kujerun wakilci a kwamitin tsaron MDD.
Mataimakin kwamishinan gudanarwar AU Thomas Kwesi Quartey, ya yi wannan kiran ne a daidai lokacin da shugabannin Afrikan ke shirin gabatar da bukatar kujerun wakilci na dindindin a kwamitin tsaron MDD, a lokacin wata ganawar shugabannin a ranakun Litinin da Talata a taron kolin AU karo na 29 Addis Ababa na kasar Habasha.
A cewar Quartey, yanayin kwamitin tsaron MDD tamkar taswira ce ta duniya baki daya, sai dai bayan yakin duniya na biyu da kuma yadda al'amura suka sauya tun daga wancan lokacin, ciki har da batun yadda Afrika ke taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya, akwai bukatar a mayar da hankali wajen baiwa Afrikar karin wakilci.
Ya kara da cewa bisa la'akari da yadda ake daukar Afrika da muhimmanci sakamakon irin rawar da AU ke takawa, ya ce da zarar Afrika ta hada kanta hakan zai baiwa nahiyar samun damar yin magana da murya guda, kuma hakan zai sa ba za'a iya yin burus da al'ummar Afrikar ba.
A shekarar 2005 ne, Afrika ta mika bukatar neman a baiwa kasashen Afrika kujerun wakilci na dindindin guda 2 da na wucin gadi 5 a kwamitin tsaron MDD domin samun iko na fada a ji a tsarin gudanarwar kwamitin tsaron MDD.(Ahmad Fagam)