Yayin taron na yini biyu, ministocin harkokin wajen kasashe mambobin AU, za su tattauna kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya da tsaro da sake fasalin tarayya da kuma batun kaura.
A jawabinsa yayin bude taron, Shugaban Hukumar kula da AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana cewa, zaman lafiya da tsaro na daya daga cikin manyan batutuwa da aka sanya gaba, inda ya ce ana bukatar sabbin dabarun tunkarar sabon salon nau'ikan rikice-rikice dake aukuwa a nahiyar.
Ya ce babu wani tashin hankali a Afrika da za a iya warwarewa ta hanyar amfani da makami, ya na mai jaddada bukatar hawa teburin sulhu da tattaunawa da kuma lalubo hanyoyin cimma mafita guda na warware matsalolin. (Fa'iza Mustapha)