Moussa Mohamat ya yi kiran ne yayin bude taron kungiyar karo na 29, da aka fara a jiya, wanda kuma zai kai ranar 4 ga watan Yuli.
An cimma yarjejeniyar bada kudin ne tsakanin kasashe mambobin AU yayin taronta karo na 27, wanda ya gudana cikin watan Yulin bara a birnin Kigali na Rwanda, inda ya mai da hankali kan samar da kudaden da kungiyar ke bukata.
Matakin da aka fara amfani da shi a watan Janairun bana, ya umarci dukkan kasashe mambobi su bada kashi 0.2 na haraji kayayyakin da kasashen da ba mambobin kungiyar ba ke shigar da su kasashensu, inda za a iya amfani da shi wajen samar da kudi ga kungiyar.
Manufar AU din ita ce, samar da nagartacciyar hanyar samar da kudade don wanzar da zaman lafiya a nahiyar ta hannun asusunta na wanzar da zaman lafiya, tare kuma da rage dogaro a kan kudaden da take samu daga abokan hulda na kasashen waje. (Fa'iza Mustapha)