Kwamishinan kungiyar ta AU mai kula da harkokin cinikayya da masana'antu Muchaga Albert wanda ya bayyana hakan, ya ce kungiyar na fatan cimma wannan buri karkashin shirin nan na yankin cinikayya cikin 'yanci ko CFTA.
Kungiyar ta hannun shirin na CFTA suna shirin bullo da kasuwar hajoji da hidimomi ta bai daya, wadda za ta rika saukaka zirga-zirgar 'yan kasuwa da masu zuba jari.
Albert ya kuma shaidawa manema labarai yayin taron kolin kungiyar AU karo na 29 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha cewa, shirin na CFTA ya hada kan kasashen Afirka 54 masu yawan al'umma sama da miliyan 1 da ma'aunin GDP da ya kai sama da dala triliyan 3.4
A shekarar 2015 ne shugabannin Afirka suka kaddamar da shirin na CFTA yayin taron kolin kungiyar AU da ya gudana a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu. (Bilkisu)