Da yake jawabi, sabon shugaban kwamitin kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya bayyana cewa ya karbi shugabancin kwamitin kungiyar ne a dai dai lokacin da nahiyar Afrika ke fama da kalubaloli masu yawan gaske, sai dai ya nanata aniyarsa na yin aiki tukuri wajen cimma muradun al'ummar nahiyar ta Afrika a tsawon wa'adin aikinsa.
Ya kara da cewa, dimbin kalubalolin da nahiyar ta Afrika ke fama da su sun hada da yawan rikice rikice, yawaitar ayyukan masu tsattsauran ra'ayi, karuwar fatara, rashin ayyukan yi, da kuma gurbacewar muhalli.
Sabon shugaban na kwamitin AU ya ce, manyan batutuwan da zai maida hankali kansu su ne, yin garambawul ga ita kanta kwamitin kungiyar ta AU, da samar da zaman lafiya da tsaro, da batun ci gaban mata da matasa, da bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar, da tabbatar da nahiyar Afrika a matsayin wani muhimmin waje da zai ja hankalin duniya baki daya.