Mahukuntan kasar Sin sun yi maraba da shawarar da hukumar lafiya ta duniya WHO ta yanke na yin watsi da wani shiri na tattauna gayyatar yankin Taiwan na kasar Sin zuwa babban taron shekara-shekara na hukumar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying wadda ta bayyana hakan yayin taron manema labarai, ta ce shawarar hukumar ta WHO ya kare martabar babban taron hukumar da kuma kudurorin babban taron kiwon lafiya na duniya, matakin da ke nuna cewa, kasashen duniya suna goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya.
Madan Hua ta kuma bayyana cewa, gwamnatin tsakiyar kasar Sin tana son duk wani taron kungiyoyin kasa da kasa da yankin Taiwan zai halartar, a rika martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya ta hanyar tattaunawa da bangarorin biyu.(Ibrahim Yaya)