Uwar gida Hua ta ce hakan, wani mataki ne da ya sabawa akidar da kasashen Sin da Amurka suka amincewa, kuma Taiwan din na yin hakan ne, domin gurgunta kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da Amurka.
Da take jawabi yayin taron manema labarai da ya gudana a Juma'ar nan, Hua ta ce wasu daga kusoshin Taiwan ne suka kitsa wannan tsari na tura tawagar, duk kuwa da cewa Sin ta sha nanata rashin amincewar ta da aikata hakan.
A daya bangaren kuma, jami'ar ta bayyana cewa ita kan ta Amurka, ta tabbatar da cewa, za ta gayyaci ofisoshin kasashen ketare dake Amurkan ne kawai, maimakon aikawa kasashe da yankuna goron gayyatar bikin rantsuwar sabon shugaban.
Kalaman uwar gida Hua na zuwa ne, bayan da wasu kafafen watsa labaru suka fidda wasu rahotanni dake cewa, tsohon kusa a gwamnatin yankin na Taiwan Yu Shyi-Kun, ya jagoranci wata tawagar wakilai daga yankin, domin zuwa birnin Washington, inda za a yi bikin rantsuwar Mr. Trump.(Saminu Alhassan)