Ya ce Sin na kan bakan ta na kin amincewa da Amurka ta yi duk wata mu'amala a hukumance, ko alaka ta soji kai tsaye da Taiwan, haka kuma ba za ta amince Amurkar ta sayar da makamai ga Taiwan ba. Wannan babban matsayi ne da gwamnatin kasar Sin ke tsayawa a kai, wanda sam ba za ta canja shi ba.
Mista An ya kuma bayyana cewa, kasar Sin na fatan Amurka zata mutunta manufar kasar Sin daya tak a duniya, da hadaddiyar sanarwa uku da aka daddale tsakanin Sin da Amurka. An ya ce, ya zama dole Amurka ta yi taka-tsantsan game da batutuwan da suka shafi Taiwan. (Murtala Zhang)