Madam Psaki ta shaidawa manema labarai cewa sanarwar RPDC na danganta ayyukan soja da aka saba yi tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu da batun yiyuwar gwaje-gwajen nukiliya bai dace ba ko kadan, tare da kimanta cewa wannan shawara wata alamar barzana ce.
"Mun bukaci Koriya ta Arewa da ta dakatar da duk wata barzana nan take, da rage neman tada kayar baya, ta kuma dauki matakan da suka dace da suka shafi kawar da makaman nukuliya, domin taimakawa komawa teburin shawarwari masu nagarta", in ji madam Psaki da ta raka sakataren kasar Amurka John Kerry a birnin Munich, bisa hanyarsa ta zuwa kasar Indiya.
Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa, KCNA ya rawaito a ranar Asabar cewa gwamnatin RPDC ta gabatar a ranar Jumma'a da wata shawara mai muhimmanci ga bangaren Amurka, dake bukatar dakatar da ayyukan soja na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Koriya ta Kudu da aka tsaida shiryawa a wannan shekara, lamarin da zai taimakawa wajen kawo zaman lafiya a wannan yanki. Ta haka, ita kuma Koriya ta Arewa za ta dakatar da gwaje-gwajenta na nukiliya. (Maman Ada)