Majalisar wakilan Amurka ta zartas da wani kudiri a ranar 3 ga watan da muke ciki, inda ya bukaci ma'aikatar harkokin wajen kasar da ta yi la'akari da ko za ta sake ayyana Koriya ta Arewa a matsayin kasar da take goyon-bayan ayyukan ta'addaci, ko kuma a'a. Idan wannan kudiri ya samu amincewa a wurin majalisar dattawan Amurka, kana shugaban kasa Donald Trump ya sa hannu a kansa, sai majalisar gudanarwar kasar za ta yanke shawara a cikin kwanaki 90.
Bayanan da tashar Intanet ta ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta nuna sun sheda cewa, Iran, Sudan da kuma Siriya, na cikin jerin kasashen dake nuna goyon-baya ga ayyukan ta'addaci. A shekara ta 2008, gwamnatin Amurka ta kawar da Koriya ta Arewa daga cikin wannan jeri, bisa wata yarjejeniyar da ta rattaba hannu tare da Koriya ta Arewa, dangane da tantance na'urorin nukiliya na Koriya ta Arewar.(Murtala Zhang)