Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya shedawa taron manema labarai cewa, MDDr ta damu matuka game da fargabar dake cigaba da karuwa a zirin Koriya, kana an bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su ninka kokarinsu wajen lalubo bakin warware matsalar ta hanyar diplomasiyya.
Ya ce gwajin makami na baya bayan nan da Koriya ta Arewa ta yi babbar matsala ce, kuma kwamitin tsaron MDD zai aiwatar da dukkan yarjeniyoyin da suka shafi wannan batu.
Ko a ranar Lahadin da ta gabata ma, sai da Koriya ta Arewa ta yi yunkurin gwajin makaminta a gabar tekun gabashin kasar, amma bai yi nasara ba, kamar yadda babban jami'in rundunar tsaron hadin gwiwa ta Koriya ta Kudu ya tabbatar da hakan. Ita ma helkwatar tsaron Amurka ta Pentagon ta tabbatar da cewa gwajin makamin na Koriya ta Arewar bai yi nasara ba.
Dama dai kwamitin tsaron MDD ya haramtawa DPRK gwajin fasahar kera makamanta masu linzami.(Ahmad Fagam)