Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Koriya ta Arewa Sin Hong-chol ya karanta sanarwar kasarsa, inda ta bayyana matsayin kasar Koriya ta Arewa game da halin da ake ciki a zirin Koriya. Sin Hong-chol ya bayyana cewa, ana gudanar da atisayen sojan da yunkurin rushe hukumomin koli da sansanin makaman nukiliya da roka da sauran na'urorin soja na kasar Koriya ta Arewa.
Don haka, hukumar babban hafsan hafsoshin sojojin jama'ar kasar Koriya ta Arewa ta bayar da sanarwa a ranar 26 ga wata cewa, za a yi amfani da sojojin musamman wajen murkushe makircin abokan gaba, kuma tana da 'yancin kai hari ba tare da yin kashedi ba, wannan ne matakin kiyaye tsaro na wata kasa mai ikon mallaka.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya bayyana a ranar 27 ga wata cewa, sanarwar da bangaren soja na kasar Koriya ta Arewa ta bayar tsokana ne. (Zainab)