in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ce ana samun karuwar adadin yara masu fama da cutuka da tamowa a Somaliya
2017-03-31 10:13:04 cri

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF ya ce, yayin da ake ci gaba da fuskantar yunwa, ana samun karuwar adadin yara da ke fama da tamowa da gudawa a kasar Somaliya.

Fiye da yara 35, 400 dake fama da tamowa ne aka samar musu abinci mai gina ciki a cibiyoyin samar da abinci mai gina jiki dake fadin kasar, a cikin watannin Junairu da Fabrerun bana. Adadin da ya karu da kashi 58 a kan na bara.

Tun daga farkon shekarar nan zuwa wannan makon, sama da mutane 18,400 ne suka kamu da matsananciyar gudawa, kuma mafi yawa daga cikinsu yara ne.

UNICEF ya yi gargadin cewa, yayin makamanciyar matsalar da aka yi fama da ita a shekarar 2011, kimanin yara 13, 000 ne suka mutu, rabin wadanda suka mutu ke nan kafin a tabbatar da matsalar a hukumance a bana.

Bayan ganawa da iyalai 'yan gudun hijira a wata cibiyar yaki da cutar amai da gudawa a garin Baidoa na kasar, Daraktar UNICEF mai kula da yankunan gabashi da yammacin Afrika, Leila Pakakala ta ce adadin wadanda suka mutun wani nau'i ne na zaburaswa don daukar matakan gaggawa.

Leila Pakakala ta ce tamowa da yunwa da kishi da kuma cuttutuka sun yi sanadin mutuwar yara, inda ta ce suna aiki ba dare ba rana tare da wasu hukumomi, domin tabbatar da ba a sake samun mutuwar yaran ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China