Wakili na musamman na babban sakataren MDD a Somaliya (SRSG) Michael Keating, ya fada cewa wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsanancin fari, lamarin da ya jefa al'ummar kasar sama da miliyan 6 cikin mummunan karancin abinci.
Keating ya kara da cewa harin na baya bayan nan ya faru ne a lokacin da kasar ke bukatar hadin kai amma ba tashin hankali ba, a lokacin da jama'ar Somaliya ke cikin matsananciyar bukata. Kasar ta fada cikin mawuyacin hali a sakamakon mummunan fari da ya afka mata, lamarin da ya haddasa mutuwar daruruwan al'umma a kasar.
Firaiministan Somaliya Hassan Ali Khaire, ya lashi takobin binciko wadanda ke da hannu a harin tagwayen boma boman a Mogadishu wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan jama'a a kalla 10.
Cikin wata sanarwar da ya fitar a Litinin din nan, Khaire ya jaddada cewa gwamnati za ta binciko wadanda ke da hannu wajen aikata laifin tare da gurfanar da su gaban shari'a.
Wata mota dauke da ababen fashewa da aka ajiye kusa da wani otel a Mogadishu da safiyar ranar Litinin din da ta gabata ta kashe mutane 7, kana wani dan kunar bakin wake ya kashe kansa a lokacin da ya kutsa cikin wata masana'anta a kusa da barikin soja a Mogadishu, inda ya kashe fararen hula biyu. Tuni kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kaddamar da hare haren. (Ahmad Fagam)