Mr.Khaire ya bayyana cewa, sabbin ministocin za su yi kokarin sauke nauyin al'umma dake wuyansu tare da bauta wa kasar.
Ya kuma kalubalanci majalisar dokokin kasar da ta gaggauta bincike da kuma zartas da jerin sunayen, ta yadda majalisar ministocin za ta fara aiki da wuri.
Shugaban Somaliya Mohammed Abdullahi Mohammed, ya yi maraba da yadda aka bayyana sunayen sabbin ministoci, yana mai cewa, zai gudanar da harkokin mulkin kasar tare da ministocin, domin kiyaye moriyar al'umma.
A ranar 1 ga watan nan ne, majalisar dokokin kasar Somaliya ta kada kuri'a, inda aka nada Hassan Ali Khaire a matsayin sabon firaministan kasar.(Lubabatu)