Ma'aikatar harkokin wajen kasar Somaliya ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta bukaci abokan huldarta na dakarun tsaron hadin gwiwa wanda Saudiyya ke jagoranta da su binciki harin da aka kaddamar a jirgin ruwan Yemen.
A kalla 'yan gudun hijirar Somaliya 33 ne suka mutu, kana wasu 29 suka jikkata a lokacin wani harin da aka kai ta sama kan 'yan gudun hijirar da yawansu yakai 150 da suke tafiya cikin jirgin ruwa a tekun Yemen a Juma'ar da ta gabata, kamar yadda ofishin hukumar bada agaji ta Red Cross dake Sanaa ya tabbatar.
Ma'aikatar harkokin wajen ta ce, wannan abin bakin ciki ne, sakamakon yadda aka kaddamar da harin kan makaurata 'yan Somaliya a kusa da tekun Hodeidah na kasar Yemen. Kana ta aike sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, da fatan Allah ya gafartawa wadanda suka mutu, sannan ta yi addu'ar samun lafiya ga wadanda suka samu raunuka.(Ahamd Fagam)