Kamfanin dillancin labarai na Saba dake karkashin ikon Houthi, ya rawaito cewa, 'yan gudun hijirar na Somali sun gamu da harin ne ta sama a daren Alhamis din data gabata, kuma ana zargin dakarun kawance wanda kasar Saudiyya ke jagoranta da kai harin.
Kawo yanzu tawagar dakarun kawancen bata ce uffan ba.
Mai magana da yawun ofishin kungiyar kare makaurata ta kasa da kasa dake Sanaa, Sheba al-Muallimy, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kungiyar bata da hannu wajen shirya tafiyar 'yan gudun hijirar na Somali a daren Alhamis.
Al-Muallimy yace, kungiyar bata da masaniya game yin bulaguron 'yan gudun hijirar sai daga bisani ne ta samun labarin cewa 'yan gudun hjirar na Somali sun yi shirin zuwa Sudan, domin tserewa tashin hankali a kasar Yemen.