Farhan Haq, mataimakin kakakin MDD ya fadawa taron manema labarai cewa, tabarbarewar al'amurran da ake fuskanta, ya faru ne a sanadiyyar karuwar tashe tashen hankula, kana ya bayyana rahoton wanda shirin hukumar samar da abinci ta duniya FAO ta bayyana game da matsalar karancin abincin dake addabar gabashi da kuma arewacin Afrika.
Haq, ya ce, baya ga matsalolin tashe tashen hankula da suka addaba yankunan, rahoton ya kuma tabo batun karancin ruwan sha, da sauyin yanayi a matsayin wasu daga cikin manyan matsalolin da suka kawo nakasu ga shirin yaki da yunwa, da samar da abinci da inganta abinci mai gina jiki wanda MDD ta kudiri aniyar cimmawa nan da shekarar 2030.(Ahmad Fagam)