Hadaddiyar kungiyar masu kula da giwaye ta Afrika AEC, ta bukaci Kungiyar Tarayyar Turai EU, da ta yi koyi da kasar Sin wajen haramta safarar hauren giwa a kasuwannin cikin gida da kuma na kasa da kasa,
AEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a Juma'ar da ta gabata, inda ta yabawa gwamnatin Sin bisa daukar wannan mataki na haramci cinikin hauren giwa, kana ta bukaci EU da ta bi sahun kasar Sin wajen hana hada hadar hauren giwaye domin ceto wannan babbar dabba daga bacewa daga doron kasa.
Shugaban kungiyar ta AEC, Patrick Omondi, ya ce sun gamsu da matakin da kasar Sin ta dauka na rufe kasuwanninta na hada-hadar hauren giwar, inda ya bayyana wannan mataki a matsayin wata babbar nasara wajen ceto rayuwa giwaye a duniya.
Omondi ya ce ya kamata EU ta yi amfani da wannan damar wanda kasar Sin ta samar na rurrufe dukkannin kasuwannin safarar hauren giwa.
Sanarwar ta AEC ta ce, alamu sun nuna cewa nan gaba kadan EU za ta bayyana matsayinta game da wannan batu na haramta cinikin hauren giwa.
Bugu da kari sanarwar ta kara da cewa, kwamitin dake lura da harkokin ciniki na kungiyar EU ya tabbatar da cewa a ranar 7 ga wannan wata da muke ciki zai gudanar da taro, inda ake sa ran zai duba wasu batutuwa da suka shafi harkokin kasuwanci kuma ana sa ran zai hada da batun cinikin hauren giwayen.(Ahmad Fagam)