Phahlane ya ce, matsayin da aka dauka game da tura 'yan sanda ba za a canza shi ba, matukar akwai bukatar hakan, domin kawar da ayyukan bata gari, da tashe tashen hankula da cin zarafi.
Wasu kungiyoyin fararen hula a kasar, sun yi ta kiraye kirayen a janye jam'an 'yan sandan daga harabar jami'o'in kasar, suna bayyana cewar tura jami'an ya sake dagula al'amurra.
Su dai daliban kasar sun fara yin bore ne, sakamakon kara kudin makaranta da mahukantar kasar suka yi tun makonnin da suka wuce. Sai dai 'yan sanda a kasar na cigaba da kokarin dakile aniyar daliban.
Hukumar 'yan sandan Afrika ta kudu ta ce, ta tura jami'anta wasu daga cikin jami'o'in kasar ne musamman wuraren da aka fara tada tarzoma domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Phahlane ya ce, tuni hukumar 'yan sandan kasar ta fara aikin sintiri a wasu daga cikin manyan makarantun kasar, sannan hukumomin gudanarwar manyan makarantun da jami'an tsaro na cikin makarantun na cigaba da daukar matakan da suka dace.(Ahmad Fagam)