Shugabar hukumar a yankin gabashin Afrika Victoria Akyeampong, ta ce rashin isashen abinci da ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai ne ya jefa 'yan gudun hijirar cikin matsanancin halin da suke ciki.
Ta ce haka batun ya ke a yankin Great Lakes, inda ke fama da rikicin siyasa, al'amarin da ta haifar da rikici tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati.
Yayin ziyarar da ta kai helkwatar kungiyar kasashen gasashin Afrika a garin Arusha na kasar Tanzania, Victoria Akyeampong, ta ce akwai bukatar samar da matakan magance rikice-rikicen
Shugabar ta hukumar kula da 'yan gudun hijira da shugaban kungiyar kasashen gasashin Afrika Liberat Mfumukeko sun amince da kafa kwamitin ko ta kwana domin ingantawa da aiwatar da matakan kungiyar na kula da 'yan gudun hijira.
Liberat Mfumukeko ya ce ya yi matukar farin ciki da matakin da suka dauka yana mai cewa, yankin ya dade yana fama da matsalar 'yan gudun hijira. (Fa'iza Mustapha)