in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron koli na dandalin Afrika da kasashen Larabawa karo na 4 a Malabo
2016-11-24 10:37:56 cri

A jiya Laraba aka bude taron koli na dandalin Afrika da kasashen Larabawa karo na 4 a Malabo, babban birnin Equatorial Guinea, inda ya samu halartar shugabanni kimanin 60 daga sassan biyu.

Taken taron na wannan karo shi ne, "hadin gwiwa don samar da cigaba mai dorewa da bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar hadin kai". Taron na wannan shekara, zai mai da hankali wajen yin nazarai game da irin nasarorin da aka cimma game da kudurorin da aka zartar a lokacin taron kolin karo na 3 wanda aka gudanar a kasar Kuwait a shekarar 2013.

Taron zai kuma tabo batun hanyoyin da za'a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Afrika da na Larabawa, don yin aiki tare wajen tinkarar manyan kalubalolin dake barazana ga shiyyoyin biyu.

Shugaban kasar Equatorial Guinea Obiang Nguema Mbasogo mai masaukin baki, ya bayyana cewa, akwai abubuwa da dama dake tabbatar da alaka ta kut da kut tsakanin kasashen Afrika da na Larabawa da suka hada da tarihi, al'adu da addini da dai sauransu.

Ya ce yana fata kasashen Afrika za su kara kokarin da suke yi wajen daukaka matsayinsu a idon duniya. Kana ya bukaci kasashen Larabawa su tallafawa kasashen Afrika wajen bunkasa cigaban fasahohi.

Taron dandalin hadin gwiwar Afrika da Larabawa an bullo da shi ne da nufin karfafa dangantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin bangarorin biyu. An kaddamar da dandalin ne a karon farko a birnin Alkahira na kasar Masar a shekarar 1977, kuma tun a shekarar 2010, ana gudanar da taron kolin ne bayan shekaru uku uku, inda ake zabar kasashen bangarorin biyu don gudanar da taron, a karo na biyu an gudanar da taron kolin ne a kasar Libya, sai kasar Kuwait a karo na 3.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China