in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya yi Allah wadai da harin bam na birnin Mogadishu
2017-02-21 10:37:46 cri

A jiya Litinin ne kwamitin sulhu na MDD, ya fidda wata sanarwa a gaban kafofin watsa labarai, inda ya yi Allah wadai da harin boma-bomai da aka kaddamar a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya, yana mai jaddada aniyarsa ta yaki da ta'addanci daga dukkanin hanyoyin da suka wajaba.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa, da kakkausan harshe, kwamitin sulhu na MDD ya yi tir da harin ta'addancin da ya faru, a wata kasuwa dake birnin na Mogadishu a ranar 19 ga wata. Harin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 39, yayin da wasu kuma suka jikkata.

Kwamitin sulhu ya nanata cewa, ta'addanci ya kasance daya daga cikin manyan kalubalolin da ke kawo wa zaman lafiya da tsaron duniya cikas, don haka ya kamata a gurfanar da wadanda suke aikata harkokin ta'addanci, da masu shirya su, da masu samar da kudi da kayayyaki, da ma masu goyon bayansu a gaban kotu.

Bugu da kari kwamitin ya jaddada cewa, ya zama dole a yi iyakacin kokari wajen yaki da ta'addanci. A sa'i daya kuma, ya nanata goyon bayan sa ga kasar Somaliya wajen neman samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali, kana da bunkasuwa. (Kande Gao

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China