Manufar shirin samun horon na kwanaki uku, ita ce ilimantar da sojojin dake aiki karkashin inuwar tawagar AMISON har ma da sojojin kasar Somliya sanin nauyin da ke kansu gami da daidaita dukkan batutuwan da suka shafi jinsi daga dukkan fannoni.
Jami'in kula da harkokin da suka shafi jinsi a tawagar AMISON manjo Bupe Chanda ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya cewa, kwas din zai taimaka wajen kawo karshen yadda sojoji ke cin zarafin mata da take hakkin bil-Adama, kana su kasance jakadun tawagar AMISON na kwarai a yayin da suke gudanar da ayyukansu. (Ibrahim Yaya)