Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin tashin bama baman. Ko da yake ana ganin cewa, reshen kungiyar Al-Qaeda dake kasar Somaliya watau kungiyar Al-shabaab, na yawan kaddamar da makamantan irin wadannan hare hare.
A ranar 8 ga wata, tsohon firaminista a gwamnatin wucin gadin kasar Mohamed Abdullahi Mohamed, ya lashe babban zaben shugaban kasar, inda kuma ake sa ran rantsar da shi a ranar 22 ga watan nan. A daya hannun kuma a 'yan kwanakin nan, kungiyar Al-Shabaab na kara matsa kaimi na kaddamar da hare-haren ta'addanci a kasar. (Maryam)