Wani jami'in dan sanda Abdullahi Ahmed, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sun tabbatar da mutuwar mutane uku, wadanda biyu daga ciki yara ne. Sannan, wasu hudu sun jikkata sanadiyyar harin da aka kai yankin Nabadda dake kusa da fadar shugaban kasar.
Wani ganau ya bayyana cewa, hare-haren sun kuma yi sanadin lalata wasu gidaje a yankin.
Wannan harin na zuwa ne, a daidai lokacin da fadar za ta karbi bakuncin bikin mika mulki, inda sabon shugaban kasar zai tare. Al'amarin da zai bada damar rantsar da shi a ranar 22 ga watan nan.
Tuni dai gwamnati ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jirage na wucin gadi, a filin jirgin saman Mogadishu, saboda rantsuwar da za a yi ranar 22 ga wata.
Kungiyar Al Shabaab ta dauki alhakin kai harin dake zuwa ne, duk da ikirarin da sabon shugaban kasar ya yi a lokacin da yake yakin neman zabe cewa, zai yaki mayakan na Al-shabaab. (Fa'iza Mustapha)