Madeira ya bayyana hakan ne cikin sharhin da jaridar Daily Nation ta kasar Kenya ta wallafa, yana mai cewa, zaben shugaba Farmajo zai taimakawa kasar Somaliya ta mance da abubuwan tashin hankalin da suka faru a baya a cikin kasar.
Kasar Somaliya ta shafe shekaru da dama tana fuskantar rashin kwanciyar hankali, da matsalar fari da tashin hankali mai nasaba da tsattsauran ra'ayi, matsalolin da jami'in na AU ya ce za su kasance tarihi biyo bayan zaben shugaban kasar da ya gudana cikin nasara.
Abdullahi Farmajo dai ya kayar da shugaban kasar mai ci Hassan Sheikh Mohamud a zaben shugabancin kasar da aka gudanar.(Ibrahim)