in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yu Zhengsheng ya gana da shugabar majalisar dokokin kasar Mozambique
2017-02-15 10:23:16 cri

Shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Yu Zhengsheng, ya gana da shugabar majalisar dokokin kasar Mozambique Veronica Nataniel Macamo, a jiya 14 ga wata a nan birnin Beijing.

Yu Zhengsheng, ya bayyana cewa, Sin da Mozambique suna raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a dogon lokaci. A shekarar bara, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Mozambique Filipe Nyusi, sun sanar da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wannan yana da babbar ma'ana a sabon yanayi. Kamata ya yi kasashen biyu su aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito, da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu, da fadada hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, da kuma kara sada zumunta a tsakanin jama'arsu. Sin tana son yin kokari tare da kasashen Afirka ciki har da kasar Mozambique, wajen aiwatar da sakamakon da aka samu a gun taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka a Johannesburg don amfanawa jama'ar Sin da Afirka baki daya.

Yu Zhengsheng ya kuma furta cewa, majalisar bada sharawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin tana son yin mu'amala tare da majalisar dokokin kasar Mozambique don ba da sabuwar gudummawa wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A nata bangare, Macamo ta nuna godiya ga kasar Sin da tallafin da Sin ta bai wa kasar Mozambique bayan da ta samu 'yancin kanta, kana Mozambique tana son ci gaba da raya dangantakar dake tsakakaninta da Sin yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China