Hukumomin lafiya a kasar Mozambique sun bayyana cewa, adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar fashewar tankar mai a tsakiyar lardin Tete na kasar Mozambique ya karu da mutane 4, bayan sa'oi 24 da ba da rahoton hadarin, kuma cikin karin wadanda suka rasa rayukan nasu har da wata mata mai juna biyu.
A halin yanzu akwai wadanda suka samu raunuka sama da mutane 60, dake kwance a asibitoci don karbar magani. Hukumomin lafiyar sun ce, akwai mutane 4 dake cikin matsanancin hali wadanda akwai bukatar a yi musu aikin tiyata don gudun kada matsalar ta sake ta'azzara.
Hukumomin asibitocin sun bayyana cewa, majinyatan na fama da matsanancin yanayin zafi, a daidai lokacin da ake kokarin ba su kulawa.
Lardin na Tete yana cikin gundumar Moatize ne inda hadarin ya afku, kuma shi ne yanki mafi zafi a kasar baki daya, a lokacin da hadin ya faru yanayin zafi a yankin ya kai digiri 37 a ma'aunin Celsius.
Madan Veronica de Deus, wata jami'a daga asibitin yankin, ta ce wasu mutane da hukumomin kasar sun ba da iyakwandishan kyauta ga marasa lafiyar.(Ahmad)