A hukuncin da ya yanke, Alkalin kotun John Mativo ya bayyana umarnin da babban sakataren ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar, Joseph Nkaissery da takwaransa na fadar shugaban kasa, Karanja Kibicho suka bayar a matsayi maras dalili.
Mativo ya ce umarnin gwamnatin na mayar da 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a sansanin da shi ne mafi girma a duniya, nuna wariya ne da ka iya janyo mayar da martini, yana mai bayyana shi a matsayin mai tsauri da bai dace ba
Ya kara da cewa, babu wata shaida da ke nuna cewa, mutanen sun taba aikata wani laifi, ko kuma kotu ta taba yankewa wani daga cikinsu hukunci, sannan babu shaidar dake cewa akwai 'yan kungiyar Al shabaab a sansanin.
Alkalin ya kuma umarci gwamnati ta dauki matakan da za su tabbatar da sashin da ke kula da 'yan gudun hijira na aiki yadda ya kamata, sannan ta kauracewa nunawa 'yan gudun hijira wariya. (Fa'iza Mustapha)