Babban daraktan zartaswar hukumar zabe da shata kan iyakoki mai zaman kanta IEBC, Ezra Chiloba ya shedawa 'yan jaridu a birnin Nairobi na kasar cewa, ya zuwa watan Disambar shekarar 2016, hukumar ta yiwa mutanen Kenya miliyan 15.9 rajistar, kana IEBC ta tantancesu.
Chiloba ya fada cewa, an fara gudanar da zagayen karshe na rajistar masu zaben ne tun daga yau Litinin, kuma ana saran za'a yiwa sabbin masu kada kuri'a miliyan 4 zuwa miliyan 6 rajistar.
Hukumar din ta IEBC ta fara aikin rajistar masu zaben ne na kwanaki 30 wanda aka fara daga ranar 16 ga watan Janairu zuwa 14 ga watan Fabrairu.
Wannan shi ne zagayen karshe na rajistar masu zaben, kafin gudanar da babban zaben kasar a ranar 8 ga watan Augasta.
Chiloba ya ce kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa duk 'yan kasar ta Kenya damar shiga a dama da su a harkokin siyasa. (Ahmad)